Wannan kudurin dokar da aka zartas jiya alhamis ya tanadi daurin shekaru har 14 a gidan kurkuku a kan duk wanda ya daura auren luwadi ko madigo a kasar.
Har ila yau, kudurin dokar ya haramta kafa kungiyoyi na 'yan luwadi tare da nuna soyayya ko wata dangantaka irin ta 'yan luwadi ko madigo a bainar jama'a.
Majalisar dattijan Najeriya ta zartas da irin wannan haramci a shekarar 2011, amma ba a san ko kudurorin majalisun guda biyu iri guda ba ne. Idan har iri guda ne, to za a mika su ga shugaba Goodluck Jonathan wanda idan ya rattaba hannu a kai sun zamo dokar kasa.
Duk da yunkurin da kungiyoyin kare muradun 'yan luwadi da madigo keyi, ana ci gaba da nunawa 'yan luwadi da madigo gaba da kiyayya da kuma kyama a Najeriya da wasu kasashen Afirka da dama.
Afirka ta Kudu ita ce kasa daya tak a nahiyar Afirka wadda ta halalta auren jinsi guda, watau aure a tsakanin 'yan luwadi da madigo, inda namiji zai iya auren namiji ko mace ta auri 'yar'uwarta mace.