Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tana Kasa Tana Dabo Abun Zai Zama Fifita Wasu Kan Wasu


Sanata Bukola Saraki, shugaban Majalisar Dattijai,
Sanata Bukola Saraki, shugaban Majalisar Dattijai,

Jami’iyyar APC, mai rinjaye a majalisun Najeriya, tace biyo bayan sulhu masamman ma da ‘yan majalisan dattawa ne yasa ta aike da jerin sunaye da take so a baiwa sauran manyan mukamai a majalisar.

Binciken da wakilin muryar Amurka Nasiru Adamu Elhikaya ya gudanar ya nuna cewa jami’iyyar tana so a nada sanata Ahmed Lawan a matsayin shugaban masu rinjaye, inda George Akume zai zama mataimakin sa, shi kuwa sanata Farfesa Shola Adeyeye ya kasance mai tsawatawa Abu Ibrahim mataimaki.

Sakataren jami’iyyar, ta APC, Mai Mala Boni, yace sun rubuta takarda wa shugaban majalisar dattawa dana majalisar wakilai, a matsayinsu na ‘yayan jami’iyyar APC, abunda suke bukatar a garesu shine su bi umarnin jami’iyya, shine abun da yanzu jami’iyya take jira daga garesu.

Dattawan dake marawa Bukola Saraki baya na ganin da jami’yyar ta basu damar zaben wadannan mukamai a tsakaninsu maimakon turo sunaye da zai zama kamar fifita wasu kan wasu.

Masanin harkokin sharia Barrister Mainasara, yace tun farko dattawan da suka zabi Bukola Saraki, basu sabawa tsarin mulkin ba sai dai rashin bin muradun jami’yya.

XS
SM
MD
LG