Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kwai Bukatar Garanbawul Domin Suyi Daidai da Tanade-Tanaden Musulunci


A cikin shekarar 2013 ne gwamnatin jihar Kano, bisa amincewar babban bankin Najeriya, ta kafa bankunan da ake kira Micro Finance Banks, a hedkwatocin kananan hukumomin jihar arba’in da hudu, da nufin bunkasa harkokin noma da kananan sanao’I, a tsakanin alumar jihar.

Ya zuwa yanzu dai wasu daga cikin sun na kokarin taka rawar gani ta fuskar sauke nauyin da aka rataya masu amma duk da haka suna fuskatar dinbin kalubale na kanranci jail da aka sa aka kafa bankunan na milyan ashiri sun yi kadan.

Farfesa, Kabir Isa Dandago, dake zaman sabon kwamishinan na jihar Kano, yace a kwai bukatar a yiwa bankunan garanbawul ta hanyar canja masu suna da tsarin aiyukansu domin suyi daidai da tanade-tanaden musulunci ko zasu samu karbuwa a idon jama’a.

XS
SM
MD
LG