Tijjani Ado Ahmad, wani matashi ne da yake kara tunatarwa da jawo hankalin ‘yan uwan sa matasa baki daya, da su yi kokari su ci gajiyar falalar wannan wata mai alfarma. Yana cewar matasa su sani da cewar wannan wata ne da duk wanda ya aiwatar da wani abu na alkhairi, to zai samu lada waddatacce da nunka abun da zai samu idan yayi wannan aiki a watan daba na ramadana ba, ashe kuwa wannan wata garabasa ce daya kamata kowane matashi yayi kokarin morarta.
Duk da sanin cewar akwai talauci a cikin jama’a to kada su karaya, suyi kokarin ganin sun taimaka a kowane hali, ba lallai sai mutun ya bada da yawa ba, koda kadan mutun ya bada to Allah zai albarkaci abun da ya bada, ya kuma wadaci wanda akaba.
Domin kuwa malamai suna kokarin kira ga al’uma, dasu kokarta wajen ganin sun taimakama masu karamin karfi, don dacewa da rahamar Allah. Babban abun nuni a nan shine duk wanda yake da tunanin wai sai yana da mai yawa sannan zai bada, to wannan hakika bashi da tunani nagari, kamata yayi ace kowane matashi nada tunanin badawa, koda kuwa yake wanda idan har ya saba da badawa to duk randa Allah yayi mishi fatahu, to zai kasance cikin masu iya badawa da yawa.
Abun nufi anan shine ka bada kadan Allah ya maida maka da maiyawa, don haka matasa kada su bari suyi kasa a gwiwa wajen taimaka ma mabukata a cikin wannan wata mai albarka, koda kuwa da karfin jikinsu ne ya kamata su yi wani abu na neman lada dama kokarin yima kasa addu’a don neman zaman lafiya, dama duk wasu matsaloli da kasa ta shiga, ko Allah ya karbi addu’oin mu albarkar wannan wata mai falala.