Ce ce ku ce da yanzu ke ci gaba da gudana kan darakata janar na tawagar gangamin yakin neman zaben da ta kai jami’iyuyar APC, ga nasara wato Rotimi Ameachi, tsohon Gwamnan jihar Rivers, masamman yankinsa na Niger Delta,
Ce ce ku cen ne dai da ake ganin na kara safafar batanci da kiyayya da kushe da kuma cewar hakan na cike da hadari mai yawa kuma yanayi ne dake ci gaba da daukar hankula game da rawar da Rotimi Ameachi, ya taka a zaben shugaba Muhammadu Buhari, a bisa dan yankinsa Goodluck Jonathan, da kuma yadda ya ci gaba dai kai gwauro da mari.
Amma kafi zabe safafar siyasar hakan ya haifarmasa da matsalar da kiyayya daga ‘yan uwansa na Niger Delta.
Kungiyar ‘yan arewacin Najeriya, mazauna yankin na Niger Delta, bisa jagorancin Alhaji Ali Kwande, ta yabawa kokarinsa a bisa nasarar da shugaba Buhari ya samu.
Alhaji Ali Kwande yace “ kwaliya ta biya kudin sabulu, kara da cewa Ameachi, ya tsaya akan wani siratsi mai karfin gaske wanda hakan yasa ‘yan uwansa suka ki shi a kan goyon bayan shugaba Buhari.