A wani sabon yunkuri na ganin an farfado da yankin arewa maso gabashin Najeriya, da hare-haren Boko Haram, ya shafa, ‘yan majaloisar dattawa da suka fito daga yankin sun kudiri anyar ganinan kafa sabuwar hukumar da zata kula da arewa maso gabashin Najeriya, hukumar da za’a yiwa lakabi da Hukumar Raya Arewa Maso Gabas.
‘Yan majalsar dattawan sun ce daukar wannan matakin ya zama wajibi ganin wadda rikicin Boko Haram, ya yi da yankin, lamarin da zai dauki shekaru.
Sanata Abdulazeez Murtala Nyako, dan majalisar dattawa dake wakiltar mazabar Adamawa ta tsakiya, a wajen wani taron tuntuba da aka yi a Yola, yayi bayanin cewa hukumar zata kula da raya yankin da kuma talafawa mutanen yakin, yana mai cewa nan da wata biyu za’a ga bayani.
Wannan na zuwa yayin da masana ke gargadin cewa a bana ana iya samun matsalar abinci a rewacin Najeriya, batun da wani masanin a harkar noma Mr. Joseph Jaru, yayi kira ga Gwamnatocin arewa da su maida hankali kan aikin gona da samar da iri mai yi da wuri.