Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Dage Zaman Shara'ar Bazoum Zuwa 7 Ga Watan Yulin 2024


Kotun Cour d’Etat a birnin Yamai
Kotun Cour d’Etat a birnin Yamai

A yau 10 ga watan Mayu, 2024 aka yi jiran jin hukuncin da kotu za ta yanke dangane da bukatar janyewa wa hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum rigar kariya, alkalan kotun sun dage zama zuwa 7 ga watan Yuni, 2024.

A ranar 5 ga watan Afrilun da ya gabata ne kotun Cour d’Etat mai ofishi a birnin Yamai ta yi zamanta na farko domin duba hanyoyin janyewa wa shugaba Mohamed Bazoum rigar kariya bayan da hukumomi suka shigar da bukatar a matsayin matakin share fagen gurfanar da shi a gaban kuliya a bisa zarginsa da cin amanar kasa.

A lokacin kotun da mai shara’a Abdou Dan Galadima ke shugabanta ta ayyana ranar 10 ga watan Mayu a matsayin ranar da za ta sanar da hukuncin da ta yanke, sai dai kuma a dan kwarya kwaryan zaman da ta yi da hantsin ranar Jumma’a, kotun ta daga sauraren karar zuwa ranar 7 ga watan Yunin gobe.

Jagoran lauyoyin hambararren shugaban kasa Me Moussa Coulibaly bai halarci zaman ba, sai dai Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Kasa Batonnier Kadri Oumarou ya halarci zaman kotun a madadin daukacin lauyoyin Nijar kuma ya yiwa Muryar Amurka karin bayani.

Magoya bayan Mohamed Bazoum wadanda suka halarci dakin shari’ar sun yaba wa matakin kotun, Intinicar Alassan wani dan gani kashenin hambararren shugaban kasar na da kwarin gwiwar doka za ta yi rinjaye a shari’ar.

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta ofishin ministan shari’a ta bukaci kotun Cour d’etat da ta janye wa hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum rigar kakiya domin ya fuskanci shari’a a bisa zarginsa da cin amanar kasa.

Yayin da magoya bayansa ke fassara matakin a matsayin bita da kullin siyasa, su kuma masu goyon bayan hukumomi na yaba wa da matakin.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG