YAMAI, NIJAR - Alkalin kotun yace ana tsare da wadanan mutane ne ba akan ka’ida ba kuma jinkirin mutunta wannan hukunci abu ne da zai ja wa gwamnatin kasar biyan tarar miliyan 1 na cfa a kowace rana har zuwa lokacin da za a bai wa wadanan mutane damar komawa cikin iyalinsu.
Tun a ranar da hukumomin mulkin sojan Nijar suka zargi hambararren Shugaban kasa Mohamed Bazoum da yunkurin tserewa daga inda yake tsare ne jami’an tsaro suka kama Abdourahamane Ben Hamey da Mohamed M’Barek a jerin mutanen da ake zargi da hannu a abinda aka kira yunkurin tada hankalin kasa da yi wa hukuma barazana.
An ja lokaci mai tsawo ba tare da jin duriyar wadanan mutane ba kafin daga bisani a gano cewa suna tsare a wani ofishin jamia’n tsaron Jandarma dake birnin Yamai lamarin da ya sa lauyoyinsu shigar da kara a kotu domin ta dubi abin da suka kira take doka da tauye hakkin bil adama.
Bayan nazari akan bahasin bangarorin biyu a zamanta na talata 2 ga watan Afrilu, kotun ta umurci hukumomi su salami wadanan mutanen.
Yace Doka ta kayyade cewa bai kamata a fice wata 1 a na tsare da mutun ba tare da an gabatar da shi gaban alkali ba. su kuma wadanan mutane sun shafe watanni 6 da mako 2 a ofishin jandarmomi abin da ke nufin ana tsare da su ne ba akan ka’ida ba.
Domin tabbatar da cewa an bi umurnin Kotun alkalin dake wannan shari’a ya gindaya wa mahukunta sharadi inji Maitre Djibo.
Yace za ta yiwu hukumomin Nijar su yi ta jan kafa kokuma su ki zartar da hukuncin kotun. matakin da ke biyo bayan aikata wannan dabi’a ta kin sakin wadanan mutane shine biyan tarar miliyan 1 na cfa a kowace rana har zuwa lokacin da komai zai je daidai.
Kawo yanzu ba wani martani daga bangaren gwamnatin Nijar wace ma’aikatar Agence Judiciare de L’etat ke wakilta a wannan shara’a koda yake hukuncin kotun na cewa akwai damar daukaka kara kafin nan da makwanni biyu masu zuwa.
A saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna