Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sun Zambaci Mata 'Yan Kasuwa Miliyoyin Nairori


Rundunar ‘yan sanda ta jihar Oyo ta damke wasu mutane da suka zambaci wasu mata ‘yan kasuwa da yawansu ya kai dari ukku, miliyoyin Nairori.

Mazambatan dai sun bude ofis ne a unguwar Adamasingba Makola, a birnin Ibadan, inda suka bukaci mata ‘yan kasuwan dasu dingi zuba Naira dubu hudu da dari biyar wasu ma fiye da haka tafkar adashi a kowace ranar Allah Ta’ala.

DSP. Kunle Ajesibutu, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, yace tuni suka kama mutane goma sha daya a cikin mazambatan da suke zargi amma suna nan suna neman shugabansu wanda ake sa ran kama shi bada dadewa ba.

Daya daga cikin matan da aka zambata Bunmi Aderogba, tace sun aike masu da sakon kattakwana cewa akwai wani taro da karfe biyu na rana, amma da misalin karfe goma sha biyu ta dago cewa abun da sakon ya kunsa yanuna cewa mutanen ‘yan 419 ne.

Idan ba’a mataba kimanin shekaru takwas da suka wuce wasu mazambata sun bullo da wani banki mai suna {wonder Bank}wato Bankin Ban mamaki, a jihar Oyo, inda suka tashi da miliyoyin Nairori na jama’a.

XS
SM
MD
LG