Maganar zaben shuwagabani a majalisa hurumin ‘yan majalisar ne Sanata Marafa Bashir Abba, dan jami’iyyar PDP, mai wakiltan mazabar Taraba ta tsakiya a majalisar dattawa ne ya bayana haka ga muryar Amurka.
Yace “ko daga wace jami’iyya ka fito kana da dama ga zabe wanda ka keso, a lokacin babu maganar jami’ya, sai dai maganar cancanta, kuma zaben da akayi kwanakin baya shine mafi yawan ‘yan majalisa suke ganin cewa ya dace domin abu ne na fahimtan juna idan aka fahimci juna dan kowane jami’yya, na iya samun mukami.”
Ya kara da cewa maganar sa baki ba zai yuba domin a cewarsa sun riga sun zabe shuwagabanin majalisa kuma babu wanda ya isa ya cire su sai ‘yan majalisa kuma sai an samu biyu bisa ukku na ‘yan majalisar kafin a cire shugaba saboda haka ka ga haka ba zai yuba.