Takaddamar ta sake dawowa kan zaben shugaban masu rinjaye da mai tsawatarwa masamman ma na majalisar dattawa biyo bayan Bukola Sarki, a matsayin shugaban majalisar wanda ya saba da muradun jami’yyar Gwamnatin APC.
Gobe talata ne ake sa ran zaben suaran shuwagabanin da har ila yau wasu ke ganin APC, na son zaben wasu da take ganin sun fi dacewa da mukaman, inda wasu dattawan ke cewa ya dace a barsu su nada shuwagabaninsu da kansu.
Bayanan bayan fagge dai yana nuna jami’iyyar na son a zabe Sanata Ahmed Lawan, a matsayin shugaban masu rinjayeGeorge Akume, ya zama mataimaki.
Sanata Danjuma Goje, dake kan gaba wajen zaben Bukola Sarki, yace ba zasu amince da sa bakin wasu da lamarin zai juye tafkar nadi ba yana mai cewa wataran ace ba sashe - sashe{ zoning} wataran ace akwai su basu san abun da ake ciki ba.