Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa, shugaban hukumar da ke kula da ayyukan ‘yan sandan kasar, Musiliu Smith ya yi murabus daga mukaminsa.
Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da ma’aikatan hukumar suka share makonni biyu suna zanga-zangar neman a kore shi.
Har ila yau ma’aikatan na kira ga hukumar EFCC ta bincike shi,
A hirar da wakilin mu Umar Farouk Musa ya yi da Hajiya Naja’atu Mohammed, kwamishiniya a hukumar ‘yan sandan, ta tabbatar da murabus din shugaban nasu.
“Da ma ka san ofis din a rufe yake, ana ta zanga-zangar cewa abubuwan da yake yi ba ya kyautawa.
A cewar Hajiya Naja’atu, an shirya za a yi taro tare da shugaban hukumar da safe amma sai bai bayyana ba, tana mai cewa hakan ya sa aka dage zaman zuwa karfe biyu.
“Da muka zo karfe biyu sai muka ga takardar cewa ya yi murabus, ya je ya kai wa shugaban kasa, kuma shugaban kasa ya ce an karbi murabus din na sa.” In ji Hajiya Naja’atu.
A kwanan nan, hukumar ta ‘yan sanda ta yi ta kai ruwa rana tsakaninta da ofishin Sufeta Janar kan wanda ke da hurumin diban mutane a aikin ‘yan sanda.
Naja’atu ta kara da cewa tuni an nada Justice Clara Ogunbiyi mai ritaya a matsayin mai rikon kwaryar shugabancin hukumar.
Saurari cikakkiyar hirar Umar Faruk Musa da Hajiya Naja'atu Muhammad: