Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kazamain Fada A Sudan Ya Kashe Akalla Mutane 36


Wata dattijiya take kada a kuri'arta a kudancin Sudan.
Wata dattijiya take kada a kuri'arta a kudancin Sudan.

Jami’an Sudan suka ce an kashe akalla mutane 36 a wani kazamin fada da ake ci gaba da gwabzawa a gundumar Abyei da ake gardama akai.

Jami’an Sudan suka ce an kashe akalla mutane 36 a wani kazamin fada da ake ci gaba da gwabzawa a gundumar Abyei da ake gardama akai,yayinda masu zabe suke ci gaba da tururuwa zuwa rumfunan zabe a wani muhimmin lamari da zai bai wa kudancin kasar ‘yancin kai.

Shugabannin kabilar Misseriya da ake alakantawa da samun goyon baya daga arewacin kasar,da kuma kabilar Ngok Dinka,da kudancin kasar ke marawa baya,litinin duk suna zargin juna kan ci gaba da tarzoma a yankin Abyei mai arzikin mai,yanki dake kan iyakar kudanci da arewacin kasar.

Wani kakakin Majalisar Dinkin Duniya,Martin Nesirky,yace sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar sun kara sintiri a yankin Abyei. Yace Majalisar ta damu kwarai kan arangamomin,kuma tana kokarin tantance yawan mutane da fadan ya rutsa dasu.

Masu fashin baki suka ce Abyei ne babbar matsala da ta rage tsakanin kudu da arewacin kasar,bayan cimma wata irin yarjejeniyar,da ta kawokarshen yakin basasar kasar, da ya dauki tsawon shekaru 21.

Da an shirya yankin Abyei zai gudanar da nasa kuri’ar tantance makomarsa lokaci daya da kudu,amma an dage shi har sai illa masha’allahu.

Ahalin yanzu kuma zaben raba gardaman yana tafiya kamar yadda ya kamata a yankin kudancin kasar. Hukumar zaben raba gardamar,tace kashi 20% cikin dari,kamar mutane dubu 750 ne ‘yan kudancin kasar suka kada kuri’a ranar lahadi,yinin da aka fara zaben raba gardamar.

Za’a ci gaba da gudanar da zaben har Asabar,kuma ana gudanar das hi cikin lumana a galibin sassa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG