Jami'an zabe a Jamhuriyar Nijar sun jinkirta zabubbukan majalisun birane da kananan hukumomi na tsawon kwanaki uku a saboda matsalolin kayan aiki.
A yanzu an shirya gudanar da wadannan zabubbukan a ranar talata, maimakon ranar asabar kamar yadda aka tsara tun da fari.
Shugaban hukumar zaben Nijar, Ghousmane Abdourahmane, ya fadawa 'yan jarida jiya alhamis cewa wasu rumfunan zabe ba su samu takardun kuri'a da wasu kayayyakin zaben ba.
Zabubbukan su ne mataki na gaba da aka tsara da nufin mayarda kasar dake Afirka ta Yamma kan turbar mulkin dimokuradiyya ta farar hula.
A watan Fabrairu ne sojoji suka hambarar da shugaba Mamadou Tandja daga kan mulki a bayan da ya sauya tsarin mulkin kasar domin kara wa'adin zamansa a kan karagar mulki.
A watan Oktoba, masu jefa kuri'a sun amince da sabon tsarin mulki wanda ya ba sojoji wa'adin zuwa ranar 6 ga watan Afrilu domin su maido da mulkin farar hula.
Kasar ta shirya gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 31 ga watan nan na janairu.