Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Borno Na Cikin Tsaka Mai Wuya - Zulum


Gwamnan Borno Babagana Zulum.
Gwamnan Borno Babagana Zulum.

Yana da matukar wahala jama’a su karbi mutanen da suka kashe musu iyaye da ‘ya’ya da sauran ‘yan uwa, haka kuma idan kuma aka ki karbar mayakan da suka tuba suka mika, suna iya komawa kungiyar ISWAP, su kuma kara yawan mayakanta a cikin daji.

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce jihar tana cikin tsaka mai wuya, a yayin da mayakan Boko Haram da dama suka tuba suka soma mika wuya.

Gwamnan ya bayyana haka ne sa’adda ya kai ziyara a garuruwan Bama da Gwoza, inda ya yi jawabi ga manyan jami’an soji da sarakunan gargajiya da kuma shugabannin al’umma.

Lokacin da gwamna Zulum ya kai ziyara fadar Shehun Bama (Facebook/ Gwamnatin Borno)
Lokacin da gwamna Zulum ya kai ziyara fadar Shehun Bama (Facebook/ Gwamnatin Borno)

Zulum ya ce shekaru 12 ana fama da yakin kungiyar ta Boko Haram, lamarin da ya sa jama’a da dama cikin ukuba ta rasa dimbin rayuka da dukiyoyi da kuma muhalli.

Ya ce “mun kasance cikin yaki shekaru 12 da suka gabata, inda muka rasa rayukan dubban mutane, haka kuma wasu dubbai har yanzu ba’a san inda suke ba, ko suna raye ko sun mutu, ba wanda ya sani. Haka kuma miliyoyin jama’a sun rasa muhallansu, yayin da manoma da ‘yan kasuwa masu arziki suka koma matalauta.”

Ya ce a yanzu da ake ganin an sami gagarumar nasara a yakin, har ta kai mayakan Boko Haram da kansu suna mika wuya, jihar na fuskantar makoma biyu masu matukar wahalar zabi.

Gwamnan ya ce yana da wahalar gaske jama’a su karbi mutanen da suka kashe musu iyaye da ‘ya’ya da sauran ‘yan uwa kai tsaye, haka kuma yana da matukar wuya ga rundunar soji da suka rasa jami’ansu da dama a yakin.

Gwamna Zulum yayin da ya kai ziyarar aiki Gwoza da Bama (Facebook/Gwamnatin Borno)
Gwamna Zulum yayin da ya kai ziyarar aiki Gwoza da Bama (Facebook/Gwamnatin Borno)

Ya ci gaba da cewa idan kuma aka ki karbar mayakan da suka tuba da ma wasu da ke da niyyar mika wuya nan gaba, hakan zai iya sa su shiga kungiyar ISWAP, su kuma kara yawan mayakanta a cikin daji, wanda kuma zai kawo cikas ga kokarin dawo da zaman lafiya a jihar.

Zulum ya ce ya zama wajibi a tsaya a nazarci lamarin a tsanake, tare da yin zabi tsakanin ci gaba da yaki ba adadi, ko kuma a hakura a karbi ‘yan ta’addar da suka tuba, duk kuwa da cewa yana da matukar wahala.

Akan haka ya bayyana cewa akwai bukatar hada hancin dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da wakilan al’ummomin da Boko Haram ta kai wa hari, domin tattaunawa da kuma Nazari, tare kuma da yanke shawarar matsaya daya akan ‘yan ta’addar da suka tuba suka mika wuya.

Wasu mayaan Boko Haram/ISWAP da suka mika wuya da makamai (Facebook/Dakarun Najeriya)
Wasu mayaan Boko Haram/ISWAP da suka mika wuya da makamai (Facebook/Dakarun Najeriya)

Mayakan kungiyar Boko Haram sun soma tuba tare da mika kan su ga jami’an tsaro, bayan kashe babban shugaban kungiyar Abubakar Shekau, a wata arangama tsakanin bangarensa da na ISWAP, lamarin da manazarta ke ganin kan iya kassara ayukan kungiyar ta Boko Haram da ta kwashe tsawon shekaru 12 tana kai hare-hare da kisan jama’a a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

XS
SM
MD
LG