Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Yobe Ya Tabbatar Da Kai Harin Jirgin Yakin Soji Kan Kauyen Buhari


Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji
Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji

Gwamnatin jihar Yobe ta tabbatar da aukuwar harin bam da jirgin saman yakin soji ya kai kan al'ummar kauyen Buhari, duk kuwa da cewa rundunar sojin saman Najeriya ta musanta aukuwar harin.

Rahotanni daga jihar Yobe da ke Arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana cewa wani jirgin saman yaki mallakar rundunar sojin saman kasar ya kai wani harin bam a kauyen Buhari, da ke cikin karamar hukumar mulkin Yunusari a jihar.

A cewar rahotanni, harin bam din na ranar Laraba wanda ake hasashen ya auku bisa kuskure, ya yi sanadiyyar salwantar rayukan mutane akalla 9, da kuma raunata wasu da dama.

To sai dai kuma da farko rundunar sojin saman Najeriya ta musanta aukuwar lamarin, a wata sanarwa da kakakin rundunar, Air Commodore Edward Gwabkwet ya fitar.

Sanarwar ta ce aiki na karshe da rundunar sojin sama ta gudanar a jihar Yobe shi ne na ranar 5 ga watan nan na Satumba, kuma ba a karamar hukumar mulkin Yunusari ba ne, haka kuma bai kunshi amfani da bam ko wani makami ba.

To amma kuma gwamnan jihar ta Yobe Mai Mala Buni, ya tabbatar da aukuwar lamarin a yau Alhamis, inda har ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar harin jirgin yakin na soji, da ke aikin yaki da 'yan ta'adda a yankin Arewa maso gabas.

A cikin sakonsa na jajen da babban daraktan lamurran watsa labarai na fadar gwamnatin jihar, Alhaji Mamman Mohammed ya fitar, gwamna Buni ya kuma umarci dukkan asibitocin gwamnati a Geidam da Damaturu, da su tabbatar da kulawa ta musamman kuma kyauta ga dukkan wadanda suka sami raunuka sanadiyyar harin.

Wannan ne ya sa rundunar sojin saman ta fitar da wata sabuwar sanarwa a yau Alhamis, inda ta lashe aman ta da ta yi a farko, tare da bayyana cewa yanzu haka an soma bincike kan musabbabin aukuwar lamarin.

Sabuwar sanarwar ta ce hakika an tura wani jirgin saman yaki domin sintiri da duba yadda al'amura ke tafiya a yankin, bayan samun wasu bayanan sirri kan ayukan 'yan kungiyar Boko Haram da ISWAP a yankin kogin Kamadougou Yobe.

Ta ci gaba da cewa jirgin ya lura da motsin wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne, da suke yi a duk lokacin da suka hangi jirgin soji yana shawagi a kan su.

"A kan haka ne matukin jirgin ya harba wasu makamai. kuma yana da kyau a sani cewa yankin ya yi suna sosai a ayukan mayakan Boko Haram," a cewar sanarwar ta soji.

Ta ci gaba da cewa "to amma cikin rashin sa'a, rundunar sojin saman sama ta sami rahotannin da ke cewa harin ya yi sanadiyyar mutuwar wasu farar hula bisa kuskure, tare kuma da jikkata wasu."

A kan haka ta ba da tabbacin cewa za'a gudanar da cikakken bincike akan musabbabin aukuwar lamarin.

Ba wannan ne karon farko da ake samun rahotannin yadda hare-haren sojoji su ke kashe farar hula ba musamman a yankin na Arewa maso gabas, inda yaki da kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram yayi kamari.

Ba da dadewa ba ne wani jirgin saman soji da ke kan hanyar dawowa daga wani hari kan 'yan Boko Haram, ya saki bam a wani ginin gida, da jama'a suke gudanar da bikin suna a jihar Borno.

Haka kuma a cikin watan Afirilun wannan shekara, wani jirgin saman yakin soji, ya yi kuskuren kai hari kan wani sansanin soji, inda ya kashe akalla jami'an soji 20.

XS
SM
MD
LG