Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Italiya, Najeriya Za Su Hada Kai Don Yaki Da Matsalar Tsaro


Manoj-Janar Massimo Biagini na kasar Italiya, hagu, tare da Manjo-Janar Anthony Omozoje, dama (Facebook/ Nigerian Army)
Manoj-Janar Massimo Biagini na kasar Italiya, hagu, tare da Manjo-Janar Anthony Omozoje, dama (Facebook/ Nigerian Army)

Italiya ta yi wa Najeriya tayin hadin kai a fannonin da suka shafi horarwa da inganta karfin sojinta.

Wata sanarwar da rundunar sojojin Najeriya ta fitar dauke da sa hannun darektan yada labarai Birgediya Onyema Nwachukwu ta ce, Babban Janar din tsaron kasar Italiya Manjo-Janar Massimo Biagini ya nemi dakarun kasashen biyu su hada kansu don yakar matsalar tsaro da ta addabi Najeriyar.

Janar Biagini ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai wa babban hafsan sojin kasa Laftanar-Janar Faruk Yahaya a hedkwatar sojin kasar da ke Abuja.

A cewar Biagini, a baya, Najeriya da Italiya, sukan hada kansu kan wasu al’amura da suka shafi horar da jami’ai yana mai cewa akwai bukatar a sake dabbaka wannan dagantaka.

Karin bayani akan: Laftanar-Janar Faruk Yahaya, Birgediya Onyema Nwachukwu, Shugaba Muhammadu Buhari, Italiya, Nigeria, da Najeriya.

Da yake na shi tsokacin, janar Yahaya, wanda ya samu wakilcin shugaban fannin tsare-tsare, Manjo-Janar Anthony Omozoje ya ce, akwai dakarun Najeriya da dama da suka amfana daga sojojin Italiya musamman a fannin horarwa.

Ya kara da cewa dakarun Najeriya, za su ci gaba da hadaka kai da cibiyoyin soji da sauran masu ruwa da tsaki, a kokarin da suke yi na ganin sun shawo kan kalubalen tsaron da ke addabar kasar.

XS
SM
MD
LG