Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Sakawa Shugabannin Kungiyar Wagner Na Mali Takunkumi


FILE - Sojojin rundunar Wagner mai zaman kanta a kasar Mali.
FILE - Sojojin rundunar Wagner mai zaman kanta a kasar Mali.

Amurka ta kakaba wa shugaban kungiyar Wagner ta Mali takunkumi, inda ta zargi sojojin Rasha masu zaman kansu da kokarin kawo cikas ga yunkurin da suke yi na mallakar kayayyakin soji da za a yi amfani da su a Ukraine, da kuma yin aiki ta Mali da wasu kasashe.

Ma'aikatar Baitulmali ta Amurka a cikin wata sanarwa da ta fitar ta zargi Ivan Aleksandrovich Maslov, wanda ta bayyana a matsayin shugaban rundunar soji ta Wagner da kuma babban jami'in kula da harkokinta da ke Mali, da yin aiki tare da jami'an gwamnatin Mali don aiwatar da aikin tura mayakan kungiyar na Mali.

“Takunkumin da baitul mali ta yi kan babban wakilin kungiyar Wagner a Mali, ya bayyana tare da kawo cikas ga wani babban jami’in da ke tallafawa ayyukan kungiyar a duniya,” in ji karamin sakataren baitul-mali mai kula da ayyukan ta’addanci da bayanan kudi, Brian Nelson a cikin wata sanarwa.

Matakin na zuwa ne bayan mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller a ranar Litinin din nan, ya ce akwai alamun Wagner na yunkurin sayan na'urorin soji daga kasashen ketare da ke samar da makaman tare da bi ta kasar Mali.

Maria Zakharova, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha, a ranar Laraba ta yi watsi da zargin na Amurka a matsayin "zagi" a wani taron manema labarai, inda ta bukaci Washington da ta yi nazari kan illar kayayyakin da sojojinta ke fitarwa.

XS
SM
MD
LG