Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra’ayoyi Sun Banbanta Kan Mutuwar Shugaban Kungiyar Wagner


Russia Prigozhin Profile
Russia Prigozhin Profile

An bayyana mabanbantan ra’ayoyi bayan rahoto kan mutuwar Shugaban Kungiyar Wagner Yevgeny Prigozhin a jiya Laraba a kasar Rasha.

Tun a shekarrar 2014 Yevgeny Prigozin dan shekaru 62 ya kafa Kungiyar sojojin haya ta Wagner, sai dai an Jima ana tafka mahawar kan inda shugaban kungiyar ya shiga tun bayan da ya jagoranci wani boren sojoji da bai yi nasara ba kan rundunar sojin kasar Rasha a watan Yunin da ya gabata.

An yi mamakin jin labarin mutuwarsa a cikin wani hadarin jirgin sama a wannan Laraba, a hatsarin da wasu shedun gani da ido suka ce, jirgin ya kama da wuta kafin ya rikito kasa. Hatsarin ya auku ne a yankin Tver da ke arewacin Mosko babban birinin kasar.

Duk da yake kawo yanzu ba a kai ga tabbatar da dalilin faduwar jirgin saman dama mutuwar shugaban kungiyar ta Wagner ba, rahotannin kan mutuwarsa sun tayar da hankulan bangarori dabam-daban, musanman na kasashen da ke da alaka da Rasha.

A hirarsa da muryar Amurka, Dr Sadik Abba mai sharhi kan harkokin tsaro da siyasar kasashen Sahel yayi tsokaci kan tasirin da mutuwar Prigozhin zai yi ga yankin. Ya ce in har an tabbatar da rasuwar Wagner a cikin jirgin da fadi, babban abun da zai damu mutanensa shine ta yaya za su shirya su cigaba da zamansu, bayan rashin maigidansu, kasancewa shi ne madorar su.

A na shi bangaren Abdourahmane Alkassoum wani mai nazari kan al’amuran tsaron yankin na Sahel, ya kawar da jita-jitan da wasu ke yi na danganta kungiyar ta Wagner da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.

Sojojin Wagner da Prigozin ke jagoranta dai sun yi kaurin suna a Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya inda suke zama da zummar yakar ‘yan tawayen da suka hana zaman lafiya a kasar. Sai dai zarge-zarge na laifukan fyade da cin zarafin fararen hula sun dabaibaiye ayyukan sojojin hayan a daya bangaren, Amurka da sauran kasashen Turai sun jima suna yar tsama da kasr Rasha ta dalilin Wagner, tun bayan bullar sojojin a kasashe kamar Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Saurari rahoton Ramatu Garba:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG