Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Aso Rock Sun Yi Atisayen Jaddada Kuzarinsu a Abuja


Dakarun Sojojin Dake Tsaron Shugaban Najeriya
Dakarun Sojojin Dake Tsaron Shugaban Najeriya

Su dai wadannan dakaru na masamman suke da alhakin gadin fadar shugaban kasa da kuma yankin Abuja

Rundunar dake tsaron shugaban kasar Najeriya, "Guard Brigade" ta yi atisayen jaddada kuzarinsu a Abuja inda har suka hau kololuwar dutsen nan na kusa da fadar shugaban Najeriya, wato Aso Rock.

Su dai wadannan dakaru na masamman sune wadanda aka dorawa alhakin gadin fadar shugaban kasa da kuma yankin babban birnin tarayya Abuja.

Su dai dakarun daga bataliyoyi guda bakwai da suka hadu suka yi birged din dake da alhakin samar da tsaro ga shugaban kasar dama babban birnin tarayyar kasar, baya ga rawar daji, kazalika sun nuna wata bajinta inda suka hau dutsen Aso Rock, mai tsawon mita 1300, inda daga can ana iya hango wajen Abuja.

Kwamandan Birged din Birgediya janar Musa Yusuf, yace hau dutsen ga rundunar a kowace shekara shine abu na karshe kuma dalili shine tabbatar da ganin cewa Sojojin a kowane lokaci suna cikin kuzari domin aiwatar da aiyukan da aka san su da shi na tsaron kasa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:59 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG