Ministan man na Nigeria Ibe Kachikwu, yace lokaci bai yi ba da za'a yi batun sayar da matattun mai ga yan kasuwa. Amma yace za;a sa bangarori masu zaman kan su wurin gyagyara da kuma gudanar da harkokin matattun man fetur.
Haka kuma za'a nemi kamfanoni kasashen waje da zasu zuba jari wurin gyagyra matattun man da kuma gudanar da harkokin su har sai an gama gyara su tsaf. Sa'anan zai je ya zanta da shugaban kasa domin tattauna ko ya dace ayi batun sayar da su.
Ministan yace har yanzu basu samu amincewar shugaban kasa na a sayar da su ba. A saboda haka bai ce za'a sayar da matattun man fetur din ba.
Tsohon Ministan mai Alhaji Umaru Dambo yace ayi taka tsan tsan domin a cewar sa sha'anin mai yana da wuya. Yace muddin kasa irin Nigeria ta sakar da hidimomin mai ga wadansu masu kwadayin kudi, to idan ba'a yi hankali ba suna iya durkusar da gwamnati
Alhaji Umaru Dambo yace ya kamata a tabbatar cewa su kafa nasu matattun man ko kuma a samu wasu kamfanoni wadanda zasu shigo. Ya zamana gwamnati tana da inda zata dafa koda tsiya zai tashi.
Yace ka san halin 'yan Nigeria, sai su zo, su ce a lalata abun tunda suna ciki a rikirkita abun ta yadda za'a maida shi banza, su zo su saya a banza.
Mataimakin shugaban yan kasuwar mai, Alhaji Abubakar Mai gandi yace suna maraba da wannan mataki.
To amma 'yan Boko suna dari dari da wannan tsari. Suna tsoron kada yan kasuwa su ci da gumin talaka.