Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ban Yi Watsi Da Kabilar Ibo Ba:Shugaba Buhari


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Zantawa kai tsaye da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi da manema labarai na ci gaba da daukar hankalin ‘yan Najeriya.

Yayinda wandansu suka bayyana gamsuwa a kan amsoshin da ya bayar kan harkokin tsaro, tattalin arziki, arangamar da sojoji suke yi da kungiyar Boko Haram, da batun masu son ballewa domin kafa kasar Biafra, Shugaba Buhari yayi dabarun kaucewa wadansu tambayoyin kai tsaye inda yafi maida hankali kan matakan da gwamnatinsa ke dauka, da farfado da tattalin arziki a yayinda darajar gangar mai ke faduwa a kasuwannin duniya.

A cikin hira da Sashen Hausa, wani masanin tattalin arziki Hashimu Mohammed, na ganin bangaren hana mu’amala da dala bai sami gamsassar amsa ba. Bisa ga cewarshi, amsar da shugaban kasar ya bayar ya nuna cewa, kamar bai san ainihin abinda ke faruwa ba, inda yace sai ya zauna da shugaban babban bankin kasar, wannan a cewarsa, babbar matsala ce kasancewa shugaban kasar ya nuna bai san abinda ke faruwa ba dangane da wannnan batu.

Wani dan kasuwar canji a babban birnin tarayya Abuja, yana ganin matakan gwamnatin shugaba Buhari zasu rusa harkokin canji. Bisa ga cewarshi, babu abinda ya shafi mutanen dake harkar canji da tattalin arzikin Najeriya, yace kamata ya yi gwamnati ta nemi hanyoyin da zata maida harkokin canji a matsayin da zai bada gudummuwa ga tattalin arzikin kasar.Yace, tattalin arzikin Najeriya ya sukurkuce ne sabili da ayyukan ma’aikatan gwamnati musamman wadanda suke ofisoshi, kama daga gwamnoni, sanatoci da sauransu.

Shugaba Buhari ya bayyana takaicin yadda ‘yan ta’adda ke daurawa kananan yara bama bamai suna kai hare haren kunar bakin wake dake jawo asarar rayuka bayan cin lagon kungiyar Boko Haram. Haka nan shugaban kasar ya yi watsi da batun nuna wariya ga kabilar Ibo, inda ya lissafa makamai da dama, kama daga shugaban babban bankin Najeriya, karamin ministan fetur, zuwa ministan kwadago da yace duk ‘yan kabilar Ibo ne.

Ga Rahoton da wakiliyar Sashen Hausa Madina Dauda ta aiko Daga Abuja, Najeriya

Nigeria-Media Chat-4"45
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:47 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG