Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria zai yi wani zaman tattaunawa da wasu yan jarida Laraban nan
Gabanin zaman da zai yi da wasu kebabbun yan Nigeria, wakilin sashen Hausa Nasiru El Hikaya ya aiko da rahoton cewa, mutane na ci gaba da magana akan yaddda suke ganin harkokin gwamnai ke tafiya ya zuwa yanzu., a daidai lokacinda kasashe masu arzikin man fetur suka fara sumulmular kudi, saboda faduwar farshin mai a kasuwanin duniya.
Dama kuwa shugaba Buhari a jawabin daya gabatar na kasasfin kudin shekara ta dubu biyu da goma sha shidda, yace gwamnatin sa zata dage wajen kwato duk kudin da wasu suka wawure. Sa'anan kuma gwamnatin sa zata maida hankali wajen tara haraji domin samun kasafin kudin daya haura triliyan shidda.
Batun soke tallafin man fetur da rage farashin litar mai da nasarar yaki da yan Boko Haram, da hana zuba kudin kasashen waje a bankuna, da hana amfani da katin dibar kudi a na'urar banki a kasashen waje, har zuwa batun arangamar sojoji da 'yan Shiya a Zaria, suna daga cikin abubuwan da ake sa ran zantawar zata tabo.
Barrista Umar Zagga wani mai sharhi akan al'amurran yau da kullum a Abuja yace idan ance an cire tallafin, sa'anan farashi zai sauko kasa. Ministan mai yace matattun mai, Kaduna ta fara aiki, Patakwal itama zata fara aiki. Sa'anan NNPC zata rika shigo da mai yan kasuwa su saya.
Masanin harkokin tattalin arziki Harun Mohammed na kwalejin kimiya da Fasaha dake Kaduna na ganin matsalar tana nan ne waje ci gaba da faduwar farashin mai. Yace basu fatar farashin mai ya ci gaba da faduwa.