Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ANYI ANFANI DA KARFI DOMIN KWACE MANI GIDAJE NA DANA GINA.


Mutane sunyi dafifi kewaye da inda daya daga cikin boma-boman ya tashi domin ganewa idanusu a Ajilari-Gomari kusa da filin jirgin sama na Maiduguri a ranar 2 ga watan Maris 2014.
Mutane sunyi dafifi kewaye da inda daya daga cikin boma-boman ya tashi domin ganewa idanusu a Ajilari-Gomari kusa da filin jirgin sama na Maiduguri a ranar 2 ga watan Maris 2014.

Tsohon shugaban majilisar dokokin jihar Kano zamanin mulkin marigayi Gwamna Abubakar Rimi Alhaji Abdullahi Abubakar Karaye yace anyi anfani da karfi wajen kwace masa gidajen sa da ya gina akan filin da marigayi gwamnan ya bashi.

Yace alhali wannan batu tana gaban kotu a bari akai karshen sharaar amma sai aka nuna fin karfi.

Su dai wadannan gidajen da ake takaddama akan su an gina su ne a wani katafaren fili da Marigayi Gwamna Abubakar Rimi ya mallakawa shi kakakin a lokacin can baya.

Sai dai kuma akwai ragowar filin da ba gin aba wanda ya zarta wanda akayi gini akan sa.

To sai dai Alhaji Aminu Dantata yayi ikirarin mallakar wannan wuri inda har ya mika takardan korafi ga rundunar yan sanda mai kula da shiya ta daya dake Kano bayan da ya fahinci an fara gine-gine a wurin.

To sai dai tun lokacin da aka fara takaddamar ne ‘Yan sanda ke gadin wannan wuri.

Sai dai a karshen makon jiya an rushe daukacin ginin dake wurin sabo da kuma tsoho.

Ga dai Mamud Ibrahim Kwari da Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG