Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An fara zabe a jamhuriyar Afrika ta tsakiya


People stand in line to cast their ballots, during elections in Bangui, Central African Republic, Wednesday, Dec. 30, 2015.
People stand in line to cast their ballots, during elections in Bangui, Central African Republic, Wednesday, Dec. 30, 2015.

An fara zabe a jamhuriyar Afrika ta tsakiya , zaben da ake kyautata zaton zai kawo karshen kusan shekaru uku na tarzoma tsakanin Kirista da Musulmi

Laraban nan aka fara gudanar da zabe a jamhuriyar Afrika ta tsakiya, zaben da aka dade ana jinkirtawa.

Mutane da dama sun baiyana fatar zaben zai kawo karshen tarzomar kusan shekaru uku tsakanin Musulmi da Kirista. Tarzomar da aka fara tun lokacinda aka yi juyin mulki a kasar a shekara ta dubu biyu da goma sha uku.

An dauki tsauran matakan tsaro sosai a zaben shugaban kasa dana wakilan Majalisar dokokin kasar da aka dage yi daga ranar Lahadi a saboda wasu matsaloli.

An girka sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a wurare masu sarkakiya. Jami'an tsaro dari uku ne suke gadi a Bangui baban birnin kasar, a yayinda yan sanda da ganduroba dubu daya da dari uku kuma suke gadin wasu yankunan kasar.

Ban Ki-moon
Ban Ki-moon

Baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon yayi kira ga masu ruwa da tsaki a kasar da su tabbata an gudanar da zaben cikin yanci da walwala da kuma lumana.

Ana sa ran cewa kusan mutane miliyan biyu ne zasu yi zabe tsakanin yan takara shugaban kasa talatin da kuma yan takara Majalisar dokokin kasar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG