Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Najeriya ta ce ta Kama Mata Uku 'Yan Boko Haram


A'isha Kabiru, Hafsat Usman Bako, zuwa Zainab Idris, daya daga cikin mata 3 da sojojin Najeriya suka kama bisa zargin cewa su 'ya;yan kungiyar Boko Haram ne.
A'isha Kabiru, Hafsat Usman Bako, zuwa Zainab Idris, daya daga cikin mata 3 da sojojin Najeriya suka kama bisa zargin cewa su 'ya;yan kungiyar Boko Haram ne.

Sojojin Najeriya sun ce sun kama wasu mata uku da suke zargin cewa 'yan ta'adda ne...

Sojojin Najeriya sun ce sun kama wasu mata uku da suke zargin cewa 'yan ta'adda ne, wadanda kuma ake zargin su na daukar mata domin su shiga cikin kungiyar.

A cikin wata sanarwar da rundunar sojojin Najeriyar ta bayar mai dauke da sa hannun Kanar Onyema Nwachukwu, an bayyana cewa sojoji sun kama hafsat Usman bako da zainab Idris da kuma A'isha Abubakar a kan hanyarsu ta zuwa garin Madagali a jihar Adamawa, daga inda suka yi niyyar shiga daji domin haduwa da 'yan'uwansu.

Sojojin suka ce Hafsat Bako, matar wani dan Boko Haram ne da sojoji suka binciki gidansa a Jimeta a shekarar 2012, suka samu bindigar AK-47 da kunshin harsasai biyu. Ya gudu ya koma Sokoto, inda aka kashe shi lokacin wani artabu da sojoji a can.

Sojojin suka ce Hafsat Bako ita ce jagorar wadannan mata wadanda ake zargin su na kuma aikin leken asiri ma kungiyar Boko Haram.

Babu wata kafa dabam da ta tabbatar da sahihancin wadannan kalamu na rundunar sojojin ta Najeriya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG