Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ba'a San Makoman Daliban Chibok Ba


Wasu iyayen daliban Chibok da aka sace.
Wasu iyayen daliban Chibok da aka sace.

Bayan kwanaki tamanin da 'yan Boko Haram suka sace daliban Chibok har yanzu ba'a san makomansu ba domin babu wani tabbas da gwamnatin tarayya ta bayar a kansu.

Jiya Alhamis daliban Chibok suka cika kwanaki tamanin a hannun 'yan kungiyar Boko Haram da suka sacesu daga makarantarsu dake garin Chibok cikin jihar Borno.

Abun mamaki shi ne babu yaran babu kuma wanda ya san makomaansu. Wannan lamarin ya dinga haifar da zullumi da tashin hankali tsakanin iyayen yaran.

Ranar 14 ga watan Afrilun shekarar nan aka sace daliban daga makarantarsu yayin da suke shirin daukar jarabawar gama karatun sakandare. Watan jiya daya daga cikin iyayen mai 'ya'ya biyu cikin daliban da aka sace ya samu bugun zuciya har ya mutu sanadiyar rashin tabbas din 'ya'yan nasa.

Tun lokacin da aka sace daliban ana tayin gangami da zanga-zanga a matakai daban-daban a duk fadin jihar Borno da wasu jihohi da ma babban birnin tarayya, Abuja na neman kubuto daliban. To amma har zuwa jiya da suka cika kwanaki tamanin da aka sacesu ba'a san inda suke ba.

Iyayen daliban sun bayyana yadda suke ji da halin da suke ciki. Sun ce har yanzu babu wani abu takamaimai akan yaran. Abun da aka fada masu da can shi ne ake cigaba da fada masu, wato za'a nemosu. Suna ganin gwamnati tana zolayarsu ne kawai. Iyayen sun rantse ba da gaske gwamnati keyi ba. Sun ce suna cikin bakin ciki domin ko kwana kwanan nan 'yan Boko Haram sun kai masu hari.

Alkawarin da shugaban kasa yayi na kai ziyara Chibok bai cika ba. Hatta kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa akan daliban bai kai ziyara Chibok din ba sai daga baya ya aika da mutane uku cikin jirgi mai saukar angulu garin Chibok inda suka yi mintuna kadan da wasu iyayen kafin su koma Abuja.

Kawo yanzu dai gwamnatin jihar Borno ta dauki nauyin karatun daliban da suka kubuta kimanin su hamsin.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00
Shiga Kai Tsaye

Labarai masu alaka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG