Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Bam Ya Fashe a Kaduna


Wani da ya samu rauni sanadiyar fashewar bam a Kaduna
Wani da ya samu rauni sanadiyar fashewar bam a Kaduna

Wani bam da ya fashe a kusa da masallacin Sheikh Dahiru Usman Bauchi a Kaduna ya jikata mutane biyu.

Bam din ya fashe ne a anguwar Asikolaye dake Kaduna. Ya jikata wasu mutane biyu kana ya tsaga gilashin motar 'yan sanda.

Wasu mazauna anguwar sun ce bam din ya fashe ne bayan sallar magariba lokacin da ake bude baki. Wani Ganao Musa Ali yace bam din ya fashe ne a gefen titi kusa da shagon wani yaron anguwar inda akan yi kasuwanci da yamma. Sai dai sa'ar da aka ci shi ne shi mai shagon ya kan rufe idan magaruba ta karato sai can ya dawo ya bude. Shi yasa lokacin da bam din ya fashe ba kowa. Ban da haka wurin na kusa da wurin kallon kwallon kafa ne.

Shi ma Babangida Abdullahi yace yana tafiya zai karasa gida sai ya ji fashewar bam. To amma babu labarin mutuwa ko kuma mummunan rauni. Bam din an saka shi ne a wata 'yar leda kusa da gidan Sheikh Dahiru Bauchi to amma ya riga ya gama salla ya koma gida shan ruwa.

Kawo lokacin rahoton jami'an tsaro sun yiwa wurin kawanya. Kwamishanan 'yansandan jihar Kaduna Mr Umar Usman yayi karin haske. Yace babu rauni ko mutuwa. Ya kira mutane su kara bada goyon baya.

Ga rahoton Isah Lawal Ikara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG