Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batun Tsige Murtala Nyako


Murtala Nyako, gwamnan Jihar Adamawa
Murtala Nyako, gwamnan Jihar Adamawa

Yanzu haka dambarwar tsige Gwamna jihar Adamawa Murtala Nyako, da mataimakinsa Bala James Ngilari

Yanzu haka dambarwar tsige Gwamna jihar Adamawa Murtala Nyako, da mataimakinsa Bala James Ngilari, ya kara tsami inda yau ‘yan majalisar dokokin jihar suka yi zama tareda aiwatar da gudurin ci gaba da wannan yunkuri.

A zaman na yau ‘yan majalisar da tun farko suka sa hannu a wannan yunkurin sun bukaci a ci gaba da batun wanda awannan karon ma kakakin majalisar dokokin jihar Ahmadu Umaru shima yasa hannu tare da goyon baya.

‘Yan majalisar, sun kuma bukaci mai rike da mukamin Cif joji jihar Ambrose Mamadi , daya kafa kwamitin mutane bakwai da zasu binciki tuhumar da ake yiwa Gwamna da mataimakinsa.

Lokaci ne kawai zai iya tabbatar da abun da zai iya faruwa ko mai rike da mukamin Cif jojin zai kafa kwamnitin ko kuma ba zai yiba.

Gwamna jihar, ta bakin kakakin yarda labarai Ahmed Sajo yace ko kadan bazu razana ba, yana mai cewa idan aka bi doka de basu da hurumin na yin abunda suke yi.

Ahmed Sajo, ya kara da cewa idan kuma suna son yin kama karya su ki bin doka da oda su sani fa cewa duk abin da dan Adam, zaiyi kararre ne in dai fararrene.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:17 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG