Al'ummar Fulani a Najeriya sun yi kira da a sama masu burtuloli a kasar domin kawo karshen tashe-tashen hankalin da ake samu tsakaninsu da manoma.
Rikicin manema da makiyaya abu ne da ya dade yana cima mahukuntar kasar tuwo a kwarya.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa Alhaji Muhammed Kirwa yace amma daga lokacin da suka gana da gwamnonin arewa su goma sha tara a kwanakin baya kisa tare da tozarta al'ummar Fulanin ya ragu kwarai. Sabo da haka suka kai ziyara jihar Neja domin yin godiya ga shugaban gwamnonin arewa Dr Babangida Aliyu wanda kuma shi ne gwamnan jihar Neja.
Alhaji Muhammed Kirwa ya kara jaddada cigaban da aka samu a wurin wanzar da zaman lafiya. Misali irin rikicin dake faruwa tsakanin Fulani da Tiv na jihar Binuwai yace yanzu wata biyu ke nan babu wani rikicin da ya taso. Sanadiyar ziyarar da suka kai jihohi yace har gwqamnan jihar Gombe ya kafa ma'aikatar kulawa da harkokin Fulani da kiwo. Haka kuma gwamnoni sun dauki matakan yin koyi da yadda gwamnan jihar Neja keyi. A wurin Sule Lamido gwamnan Jigawa, yace sun samu canji daga lokacin da suka yi taronsu.
Dangane da alkalin kotun musuluncin nan da ya sayar da kaddarorin wasu Fulani a Zungeru jihar Neja wai ya biya diya, shugaban kungiyar Miyetti Allah yace suna sane da maganar. Kawo yanzu sun gamsu da matakan da aka dauka. Yace gwamnan jihar yana sane da maganar. Gwamnan ya kira a dauki matakan mayar ma Fulanin da hakinsu. Shugaban yace suna son a biya mutanen diya daidai gwargwadon kayansu da aka sayar. Suna nan sun sa ido su ga menene za'a yi bayan alkawarin da gwamnan yayi.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari