Domin bin dig-digin maganar abokin aiki ya zanta da Alhaji Awal jami'in kungiyar kare hakin bil adama wanda ya kara haske. Jami'in ya tabbatar cewa abun dake cikin rahoton yana daya daga cikin abubuwan da suka gano ma idanunsu. Ya ce sojojin Najeriya ko jama'an kasar idan sun kama wadanda suke zargi 'yan Boko Haram ne basa gurfanar dasu gaban sharia. Wasu ma da ba 'yan Boko Haram ba ne ana kamasu a nemesu a rasa. Kawo yanzu suna da koke-koke da dama kan wadanda sojoji suka kama amma ba'a san inda suke ba. Iyalansu basu san inda suke ba kuma sojoji basu bada bayyanin inda suke ba.
Misali a Maiduguri da suka je sun hadu da 'yanuwan wadanda aka kama kuma babu labarin inda suke. Mahukunta basu bada bayanin laifin da suka yi ba da inda suka aikata laifin. A Yobe an kama wani shugaban 'yan kasuwa kusan shekara daya da ta gabata amma shiru ake ji kamar an shuka dusa. Babu bayaninsa. An nemeshi an rasa.
Tunkarar hukumomin sojoji ya yi wuya domin suna kallon kowa tamkar dan kungiyar Boko Haram ne kuma mugun makiyi. Ya ce babu doka takamaimai da zata yi maganin ta'adanci. Sabili da haka kungiyar ke kokarin ba gwamnatin Najeriya shawara ta fito da dokokin da zasu magance ta'adanci domin sojoji sun san ba zasu iya maganin abun dake faruwa ba.
Batun cewa sojoji sun harbe wadanda suka kama ko suka sassaresu ko suka harbe kafafunsu Alhaji Awal ya ce su sojojin da kansu suka tabbatar sun kashe mutane wadanda Amnesty International ta kiyasta sun kai 950 ko fiye da hakan. Ya ce da zara an yi zargin cewa wani dan Boko Haram ne sai su harbeshi.
Ga karin bayani.