Kungiyar Amnesty International ta ce tana da shaidar wadannan kashe-kashen.
A cikin rahotyon da ta bayar talata, kungiyar ta Amnesty ta ce "bayani mai tushe" da ta samu daga wani babban hafsan sojan Najeriya ya nuna cewa mutane fiye da dari tara da hamsin (950) wadanda ake zargin su na da alaka da kungiyar Boko Haram, sun mutu a hannun sojojin a cikin watanni 6 na farkon wannan shekara.
Kungiyar Boko Haram tana ikirarin cewa tana so ne ta kifar da gwamnatin Najeriya ta maye gurbinta da mai bin tafarkin Islama. Kungiyar ta kashe ko ta haddasa mutuwar mutane masu yawan gaske.
Kungiyar Amnesty International ta ce fursunonin da aka kama ana gana musu azaba, kamar shake su har su mutu, ko barinsu su mutu da yunwa, ko kuma ana kashe su kai tsaye a wannan farmakin da sojoji ke kaiwa a yankin arewa maso gabashin kasar.
Kungiyar ta ce manyan jami'an ma'aikatar tsaron Najeriya sun kasa bayar da amsar rubutattun bayanai da ta mika musu a kan wani lamarin da ya faru ranar 19 ga watan Afrilu, lokacin da sojoji suka je suka jibge gawarwakin mutane 60 a dakin ajiye gawa na asibitin garin Damaturu a Jihar Yobe, su na ikirarin cewa an kashe su ne a musanyar wuta.
Amma wata majiya, ta fadawa kungiyar Amnesty International cewa gawarwakin na wasu mutane ne da aka kama, aka fito da su daga dakunan da ake tsare da su ciki, aka harbe su baki daya.
Kungiyar ta ce wasu fursunonin kuma sun mutu a cikinw asu munanan halaye ko dai na rashin iskar shaka, ko an bar su da yunwa har suka mutu.
Rundunar sojojin Najeriya ta sha musanta zarge-zargen cewa dakarunta su na keta hakkin bil Adama.