WASHINGTON, D. C. - Shugaban rikon kwarya, Mahamat Deby Itno, ya sanar da mutuwar sojojin a ranar Litinin a shafukan sada zumunta. Hukumomin kasar Chadi sun ce suna zargin mayakan Boko Haram daga Najeriya ne suka kai harin, lamarin da ke kara nuna damuwa game da karuwar tashe-tashen hankula a kusa da kan iyakar.
Kungiyar Boko Haram ta kaddamar da ayyukan ta’addanci fiye da shekaru goma da suka gabata kan ilimin boko tare da neman kafa shari'ar Musulunci a arewa maso gabashin Najeriya.
Rikicin ya bazu zuwa kasashen yammacin Afirka da suka hada da Kamaru, Nijar da kuma Chadi. Sama da mutane 36,000 ne aka kashe musamman a Najeriya a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Deby Itno ya kwace mulki ne bayan da aka kashe mahaifinsa, wanda ya mulki kasar sama da shekaru 30, yana yakar 'yan tawaye a shekarar 2021.
-AP
Dandalin Mu Tattauna