ABUJA, NIGERIA - Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar da daraktan labaru da hulda da jama'a na hedkwatar mayakan saman, Air Commodore Edward Gabkwet ya sanya hanu a kai ranar Litinin.
Tunda farko dai an lura yan ta'addan na loda jarkokin mai a wasu motocin yaki na ‘yan ta'addar a wurin da aka yi amanna babbar cibiyar ajiyar kayayyakin ‘yan ta'addan ne.
Wannan ya sa aka ta da jiragen yaki wadanda suka yi ruwan wuta a wadannan sansanoni kuma suka kone wuraren kurmus tare da hallaka ‘yan ta'addan da ke wurin da kuma lalata motocin da aka girke masu manyan bindigogin harbo jiragen sama.
Jiragen yakin kazalika sun kuma hango wasu motocin a kori-kura dauke da manyan makamai da mayaka na nufowa wurin, inda nan take suma aka harba masu bama-bamai aka tarwatsa su.
Sojojin Najeriyar sun kara nanata kudirinsu na ci gaba da tabbatar da tsaro ne a Arewa maso Gabas da ma sauran sassan Najeriya daban-daban.
Dandalin Mu Tattauna