An dai mika su ne ga ministan kula da walwalar jama'a na kasar Chadi Hon. Abdoullaye Mbodou Mbam,i a garin Bagasola a wani bangare na irin hobbasa da rundunar MNJTF din da gwamnatocin shiyyar keyi na karfafa gwiwar yan ta'addan su ajiye makami.
Kwamandandan sashi na biyu na dakarun kawancen Manjo Janaral Itno ya nemi sauran mayakan Boko Haram din da ke cikin daji da su yi koyi da wadannan sama da arba'in din da su ka yi saranda.
Kwamandan kazalika ya kuma nemi sarakunan gargajiya da sauran shugabannin al'umma da su ci gaba da taka rawa wajen yakar tsattsauran ra'ayi da ke zama makamashin ta'addanci a yankin.
A cewar wani masanin tsaro Farfesa Mohammed Tukur Baba lalle wannan mika wuya da yan ta'addan ke yi dayan biyu ne, imma ko don irin ruwan wuta da dakarun yankin ke masu ba kakkautawa ko kuma sun gaji da tada kayar baya da rayuwa cikin kunci a cikin daji.
Dandalin Mu Tattauna