CHAD - Tuni dai Tarayyar Turan ta mikawa wani kwararren baturen kasar Faransa alhakin jagorantar wannan babban aiki da ake sa ran zai lashe zunzurutun kudi har Euro miliyan shida,
Dama dai Tarayyar Turai na tallafawa wajen yaki da ta'addanci da kuma tsatsauran ra'ayi baya ga taimakon da take ci gaba da baiwa rundunar dakarun kawancen kasashen yankin tafkin na Chadin.
Ganin har yanzu mayakan na Boko Haram da suka karkasu gida-gida na ci gaba da tafka aika-aika, ya sa ake ganin cewa yanzu lokaci ya yi da za a fuskanci hakan.
Masanin tsaro da zamantakewa, Farfesa Mohammed Tukur Baba ‘Dan Iyan Mutum Biyu na mai cewa ai kuwa lokaci ya wuce amma kafin a yi hakan sai gwamnati ta nuna karfi ta kuma nuna ita ke da iko ba wai ace za a lallabe su ba.
Tun tuni dai daidaikun kasashen tafkin na Chadin suka kakkafa cibiyoyin sake tsugunar da tubabbun mayakan na kungiyar Boko Haram.
A cewar tsohon babban kwamandan rundunar kasashen yankin tafkin Chadin, Janar Abdou Ousmane, ba shakka an karya lagon Boko Haram sai dai har yanzu da ‘dan sauran rina a kaba.
Amma a bangaren shugabannin kasashen sun nuna gamsuwa da irin rawar da sojojin nasu ke takawa, harma sun aike da sakon jinjina ga rundunar ta MNJTF.
Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:
Dandalin Mu Tattauna