Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojin Najeriya 3 Da 'Yan Sanda 4 Sun Mutu Sakamakon Kwanton Baunan 'Yan Bindiga A Zamfara


Sojojin Najeriya 3 da jami'an 'yan sanda 4 suka hallaka yayin da suke kokarin dakile harin 'yan bindiga akan babbar hanyar Zamfara a yau Alhamis.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Muhammad Dalijan, ya bayyana cewa 'yan bindigar na shirin kaddamar da hari a kan wani kamfanin gine-gine dake kan babbar hanyar.

Ya cigaba da cewa, nan take rundunar tsaron hadin gwiwa da ta kunshi jami'an 'yan sanda da sojoji suka zabura zuwa wurin, sai dai an 'yan bindigar sun yi musu kwanton bauna tare da bude musu wuta.

Kwamishinan 'yan sandan ya kara da cewa dakarun sun nuna jarunta a kokarin dakile harin.

"Suna cikin tafiya sai suka gamu da turjiya daga 'yan bindigar, tare da yin musayar wuta dasu wanda a sakamakon hakan muka rasa wasu daga cikin jami'an soja dana 'yan sanda."

"Muna tabbatar da mutuwar sojoji 3 da 'yan sanda 4", a cewarsa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG