Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Najeriya Da Aka Tasa Keyarsu Daga UAE Sun Isa Abuja


Filin Jiragen Sama a Abuja
Filin Jiragen Sama a Abuja

Mutanen da aka dawo da su daga Hadaddiyar Daular Larabawan sun hada mata 90 da maza 310.

Jami’ai daga ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro tare da hadin gwiwar hukumar kula da ‘yan gudun hijira, da bakin haure da kuma ‘yan gudun hijira na cikin gida (NCFRMI) da hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) da kuma Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), da sauran masu ruwa da tsaki ne suka tarbe mutanen a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Mutanen da aka dawo da su daga Hadaddiyar Daular Larabawan sun hada mata 90 da maza 310.

Wannan korar dai na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin diflomasiyya ke ci gaba a tsakanin kasashen biyu, wanda ka iya samo asali daga wasu batutuwa da ba a bayyana ba.

Duk da haka, rahotanni a farkon wannan shekarar sun nuna cewa kasashen biyu sun cimma yarjejeniyar dage takunkumin tafiye-tafiye da aka yi wa 'yan Najeriya.

Gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa a watan Yulin 2024 ta sanar da cewa ta dage takunkumin hana shiga kasar da ta kakaba wa ‘yan Najeriya nan take.

Gabanin dage takunkumin, kamfanin jiragen saman Emirates ya bayyana cewa zai cigaba da ayyukansa a Najeriya tun daga ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa, inda zai fara zirga-zirga tsakanin biranen Legas da Dubai a kullum.

A cikin Yuni, bayan tattaunawa da dama da hukumomin UAE, gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa ‘yan kasar cewa nan ba da dadewa ba za a dage haramcin biza.

A dai dai wannan lokaci ne kuma aka bayyana cewa Najeriya ta biya kashi 98 cikin 100 na dala miliyan 850 da ake bin kasar, lamarin da ke nuna an samu ci gaba wajen warware takaddamar.

-Punch-

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG