An yankewa ma’aikaciyar jinya ‘yar Najeriya, Ruth Auta, mai shekaru 28 dake zaune a Burtaniya daurin shekaru 3 a kurkuku saboda sakacin da yayi sanadiyar mutuwar jaririnta mai makonni 10 da haihuwa, Joshua Akerele.
Shari’ar wacce ta ja hankula da dama, ta samo asali ne daga gazawar Ruth Auta ta baiwa jaririnta kulawar da ta dace yayin da take aikin kwana a asibitin Royal Bolton.
Al’amarin ya faru ne a ranar 20 ga watan Disambar 2022, lokacin da aka bada rahoton cewa Ruth Auta ta bar jinjirinta babu mai kula dashi a dakin hutawar ma’aikatan jinya tsawon sa’o’i 8 da take bakin aiki.
binciken da aka gudanar akan gawar ya bayyana cewar tsananin zafi ne ya hallaka shi saboda baya ga kayan sanyin da aka sanya masa an kuma lullube shi da manyan barguna, dalilan da suka sabbaba mutuwarsa.
A hukuncin da ta zartar, mai shigar da kara ta gundumar Crown, Sara Davie, ta jaddada girman sakacin Ruth Auta da kuma cin amanar data yi, inda tace, “a matsayinta na jami’ar jinya, kamata yayi Ruth Auta ta san irin hatsarin dake tattare da barin jinjirinta ba tare da mai kula ba.
“Gazawarta wajen bada kulawa da kuma yunkurinta na gujewa shari’a sun nuna rashin nadamarta”
Dandalin Mu Tattauna