Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 30 Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka A Maiduguri - NEMA


This aerial view shows houses submerged under water in Maiduguri on September 10, 2024.
This aerial view shows houses submerged under water in Maiduguri on September 10, 2024.

Kakakin hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) Ezekiel Manzo ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “adadin wadanda suka mutu ya kai mutum 30”,

Mummunar ambaliyar da ta afkawa birnin Maiduguri dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya tayi sanadiyar asarar akalla rayuka 30, sannan ta tilastawa mutane dubu 400 barin muhallansu, a cewar hukumomi a jiya Laraba.

Kakakin hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) Ezekiel Manzo ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “adadin wadanda suka mutu ya kai mutum 30”, kwana guda bayan da ruwa daga wata madatsar ruwa da ta tumbatsa tayi awon gaba da dubban gidaje a babban birnin jihar borno.

“Halin da ake ciki a Maiduguri na da razanarwa”, a cewar wata abokiyar aikin Manzo na NEMA mai suna, Zubaida Umar.

“Ambaliyar ta mamaye kimanin kaso 40 cikin 100 na ilahirin birnin. Hakan ta tilastawa mutane barin gidajensu, gasu nan a warwatse a ko’ina.”

“Daga kididdigar da muke da ita, akwai mutane dubu 414 da suka rasa gidajensu, “har ila yau “adadin na iya kaiwa miliyan guda.”

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa a shafinta na x a talatar data gabata cewar, ambaliyar ita ce mafi muni da aka gani a birnin maiduguri a cikin shekaru 30 da suka gabata.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG