Jam’iyyar PDP taki amincewa ta sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar zaben gwamnan jihar Edo da aka shirya gudanarwa a ranar 21 ga watan Satumbar da muke ciki.
Tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Abdulsalam Abubakar ne ya bayyana hakan a yau Alhamis a wurin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar a birnin Benin.
A cewarsa, PDP tace za ta amince ta rattaba hannu kan yarjejeniyar ne kawai idan har an cika wasu sharudda.
Ya kara da cewar, “na gana da gwamnan jihar a jiya kuma ya shaida min cewar jam’iyyar PDP ba za ta sanya hannu kan yarjejeniyar ba.”
“Yace mataukar aka cika wadannan sharudda, zamu zo Abuja mu sanya hannu kan yarjejeniyar.”
Duk da cewar PDP da dan takararta a zaben, Mr. Asue Ighodalo, basu sa hannu akan yarjejeniyar ba, sauran jam’iyyu ciki harda APC da dan takararta, Monday Okpebholo da takwaransa na jam’iyyar Labour, Olumide Akpata, sun rattaba hannu akanta.
Dandalin Mu Tattauna