Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zamfara: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Matafiyan Da Ba A San Adadinsu Ba


Yan bindiga
Yan bindiga

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, yace an tura karin jami’ai musamman ‘yan sandan kwantar da tarzoma zuwa yankin domin su bude hanyar.

‘Yan bindiga dauke da muggan makamai sun tare babbar hanyar Gusau zuwa Funtua, tare da yin awon gaba da matafiyan da ba’a san adadinsu ba.

Wani matafiyin dake makale a yankin, Yusuf Tsafe ya sahidawa tashar talabijin ta Channels cewar, da sanyin safiyar yau Alhamis ‘yan bindigar suka yiwa babbar hanyar tsinke tare da kafa shinge a yankin Tazame na hanyar.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun zo da yawan gaske da kimanin babura 50, kowane dauke da mutane 3, inda suka sace matafiyan da ba’a san adadinsu ba.

Shima wani matafiyan na daban ya tabbatarwa tashar talabijin ta Channels cewa, da safiyar yau Alhamis ‘yan bindiga sun tare hanyar Magazu zuwa Kucheri wacce ita ma ta hadu da babbar hanyar Gusau zuwa Funtua.

Ko da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, yace an tura karin jami’ai musamman ‘yan sandan kwantar da tarzoma zuwa yankin domin su bude hanyar.

Zamfara na cikin jerin jihohin arewa maso yammacin Najeriya dake fama da kungiyoyin ‘yan bindiga, wadanda ke sace dimbin jama’a domin neman kudin fansa tare da sace dukiya da kona gidajen al’umma.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG