A yakin neman zabe da ya kai jihar Filato, Goodluck Jonathan ya kuma yi alkawarin inganta harakar noma musamman noman rani domin matasa su sami ayyukan yi.
Shugaban jam'iyyar PDP na kasa Alhaji Adamu Mua'zu ya bayyana nasarorin da shugaban kasan ya samu wadanda suka hada da kawar da cutar ebola. Ya bukaci jama'ar jihar Filato su zabi jam'iyyar PDP ba tare da banbancin kabila ko addini ba.
Shi ko Namadi Sambo mataimakin shugaban kasar ya yiwa al'ummar jihar albishir kan jirgin kasa da zai fara sufuri a mako mai zuwa daga birnin Jos zuwa sassa daban daban.
Amma gwamnan jihar Filato Jonah Jang kira yayi wa shugaban kasar ya umurci hukumar zabe ta amincewa jama'a su yi anfani da katin zabe na wucin gadi a zabe mai zuwa kasancewar yadda jama'a da dama basu samu katin din-din-din ba.
Mataimakin shugaban kemfen din Jonathan na shiyar arewa Kabiru Tanimu Turaki yace alkwarin da suke son jama'a suyi masu shi ne ranar 14 ga watan gobe zasu ba PDP kuri'unsu. Yace Filato gidan PDP ce. A jihar aka haifi PDP a jihar kuma ta girma har aka yayeta.
Ga rahoton Zainab Babaji.