Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siyasar Bangaranci Ko Addini Ba Ta Da Amfani - Matasa


Taron Matasa Na Zauren VOA
Taron Matasa Na Zauren VOA

Yayin da ake ci gaba da tunkarar zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi a Najeriya, matasa, kungiyoyin fafutuka da wasu masu ruwa da tsaki a harkokin zabe da siyasa sun yi jan hankali ga 'yan kasar musamman ma matasa da su nisanci duk wani wanda zai jawo su cikin yanayi na bangar siyasa.

ABUJA, NIGERIA - Masu ruwa da tsakin dai sun yi kira ga ‘yan Najeriya ne da su gujewa siyasar bangaranci, kabilanci ko addinni a yayin taron zauren VOA na matasa da ya gudana a birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin babbar manaja edita, Grace Alheri Abdu.

Wannan taro dai na zuwa ne ‘yan makonni biyo bayan gudanar da makamancinsa da ya gayyaci mata wadanda ke neman takarar siyasa a matakai daban-daban a fadin kasar.

A yayin jawabi bayan taron, shugaban kungiyar fafutukar kare hakkin fararen hula wato CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani, ya ce taron na zauren VOA ya zo a daidai gabar da ake bukatarsa ganin yadda da dama mutane ke raba kan al’umma, suke neman ci gaba da kawo siyasar kabilanci, bangaranci da addini, ya na mai cewa kar matasa su yarda a ba su kwaya a yi bangar siyasa da su.

Ambassada Eniola Cole, babbar daraktar kungiyar NESS Action mai fafutukar wayar da kan matasa a game da siyasa, tattalin arziki da sha’anin tafi da tsare-tsaren gwamnati, wacce ta yi bayani a kan aikin kungiyarsu, ta yi kira ga matasan Najeriya da su fito kwansu da kwarkwatarsu a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi da aka daga zuwa ranar 18 ga watan Maris da muke ciki, su jefa kuri’arsu tare da tabbatar da sa ido a kan yadda za’a kirga kuri’un da sanar da sakamakon zaben, su kuma yi bibiya ga ayyukan gwamnati bayan zaben.

Taron Matasa Na Zauren VOA
Taron Matasa Na Zauren VOA

Shi ma Kwamared Sa’idu Sambo Kaftan, shugaban gidauniyar tallafawa ilimin yara a Arewacin Najeriya ya bayyana cewa, fatansa shi ne matasan kasar su zama ingantattun matasa kamar yadda yake gani a kasashen turai yana alakanta irin ci gaba da ake gani a kasashen turai da yanayin jagoranci da ake bayarwa tun lokacin tasowar ‘yan kasashen.

A wani bangare kuma, mukaddashin darakta mai kula da harkokin zabe a birnin tarayya Abuja, Malam Garba Ali Ishaq, ya ce bayanan da aka gabatar a taron matasa na zauren VOA na da muhimmancin gaske ganin yadda hakan zai taimaka wajen jawo hankalin matasan a kan yadda za su yi zabe ba tare da sun yi bangar siyasa ba.

Ya kara jaddada cewa, hukumar INEC na ci gaba da wayar da kan al’umma kan muhimmancin su fito su yi zabe la’akkari da yadda aka ga mutane ba su wani fito ba don jefa kuri’arsu a zaben shugaban kasa da ya gabata.

A yanayin da ake ciki dai, masana siyasa na ci gaba da yin kira ga masu kada kuri'a musamman wadanda suka yi a karon farko kuma matasa a kasar da kada su karaya bayan ganin sakamakon zaben shugaban kasa ko kuma don ‘dan takarar da suka zaba bai sami nasara ba domin kuwa za’a gudanar da zabukan gwamnonin jihohi da ‘yan majalisun dokokin jihohi masu muhimmanci a ranar 18 ga wannan wata da muke ciki, biyo bayan dage zaben da hukumar INEC ta yi saura kwanaki 3 a gudanar da zaben.

Masanan sun kuma kara da cewa, zaben na gwamnonin jihohi na da muhimmancin gaske ga al’umma ganin cewa, su ke gina makarantu, asibitoci, hanyoyin cikin gari kuma su ke da alhakin samar da hanyoyin sufuri da sauran muhimman ayyuka a kasa.

Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:

Siyasar Bangaranci Ko Addini Ba Ta Da Amfani - Matasa.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:17 0:00

XS
SM
MD
LG