Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Tsaron DSS Ta Ce Ta Gano Wani Shiri Na Kawo Rudu Bayan Zaben Gwamnoni A Najeriya


Dr. Peter Afunanya
Dr. Peter Afunanya

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta ce ta gano wani shirin boye da wasu mutane ke yi don kawo rudu da tabarbarewar doka da oda a kasar jim kadan bayan gudanar da zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi da aka shirya yi ranar 11 ga watan Maris.

Wata sanarwa da kakakin hukumar tsaron DSS Dr. Peter Afunanya ya tura wa muryar Amurka, ta ce hukumar ta tura sakon gargadi mai zafi ga ‘yan siyasa da magoya bayansu, akan su yi hattara su kuma guji yada labaran karya, da kalaman batanci, da sauran kalamai marasa ma'ana da ka iya tada zaune tsaye tunda siyasa ba harkar ko a mutu ko ai rai ba ce.

Hukumar DSS ta ce wasu ‘yan siyasa na kokarin haddasa zaman dardar a wasu sassan kasar gabanin zaben gwamnoni da bayan zaben, duba da yadda wasu ‘yan siyasar ke caccakar junansu, lamarin da ta ce na da matukar hadari ga tsaron kasa.

Hukumar ta DSS ta kuma ce babu wata hujja da wani dan siyasa ke da ita ta daukar doka a hannu, maimakon haka kamata yayi duk wani mai korafi ya garzaya kotu don neman a bi masa hakkinsa.

A dangane da zaben gwamnoni da za aka shirya yi a karshen wannan makon amma aka dage, DSS ta jaddada cewa ta shirya don tabbatar da tsaro tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro don dakile duk wani yunkurin tada zaune tsaye a lokacin zaben.

Hukumar ta DSS ta tabbatar da cewa za ta yi aiki wurjanjan don kare zaben da masu zabe, kuma ba za a bari a yi kafar ungulu ga harkar zaben ba a fadin Najeriya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG