WASHINGTON, D. C. - Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Cameron ya shaida wa BBC a ranar Litinin cewa, Birtaniya ba ta goyon bayan wani mayar da martani na ramuwar gayya, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Paris za ta yi kokarin shawo kan Isra'ila cewa kada ta mayar da martani domin hana karuwar rikicin.
Harin da Iran ta kai a ranar Asabar, kasa da makonni biyu bayan wani harin da ake zargin Isra’ila ta kai a Syria, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu jami’an Iran a wani ginin karamin ofishin jakadancin Iran, shi ne karon farko da Iran ta kaddamar da farmakin soji kai tsaye kan Isra’ila, duk kuwa da cewa sun dade suna kiyayya da ta shafe shekaru da dama ana yi tun lokacin juyin juya hali na 1979.
Kakakin sojin Isra'ila ya ce kashi 99 cikin 100 na makaman da Iran ta harba an dakile su.
Isra'ila da Iran suna zaman dar-dar da juna tsawon watanni shida tun da farkon yakin da Isra'ila ta fara da mayakan Hamas a zirin Gaza. Yakin ya barke bayan da kungiyar Hamas da ke samun goyon bayan Iran, suka kai wani mummunan hari a kan iyaka a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 1,200 a Isra'ila tare da yin garkuwa da wasu karin 250.
Bayan nan harin da Isra'ila ta kai a Gaza ya haifar da barna mai yawa tare da kashe mutane sama da 33,700, a cewar jami'an kiwon lafiya na yankin.
-AP
Dandalin Mu Tattauna