Isra'ila ta fada a ranar Lahadi cewa Iran ta harba mata makamai guda 320, a wani hari da ba a taba ganin irinsa ba a baya, amma makaman kariyarta na sama da kuma na Amurka da sauran kasashe dake goyon bayan Isra’ila sun kakkabo kashi 99 cikin 100 na makaman.
"Sun gaza a harin da suka kai," abin da Laftanar Kanal Peter Lerner, mai magana da yawun rundunar tsaron Isra'ila, ya fada wa gidan talabijin din CNN kenan.
Lerner ya ce Tehran ta kai hari kan wani sansanin soja da Iran ta ce an yi amfani da shi wajen kai harin ranar 1 ga watan Afirilu akan karamin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus babban birnin kasar Syria, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu janar-janar na Iran guda biyu. Lerner ya kuma ce hare-haren da aka kai a cikin dare "basu yi barna ba sosai."
Kakakin rundunar tsaron Isra’ila ta IDF ya ce Iran ta harba jiragen sama marasa matuki dake dauke da ababen fashewa guda 170 kan Isra'ila, da makamai masu linzami samfarin ballistic guda 120 da kuma wasu guda 30, inda yawancinsu suka fito kai tsaye daga yankin Iran, ko da yake, wasunsu kuma mayakan da ke samun goyon bayan Iran da ke Iraki da Yemen ne suka harba su.
A halin da ake ciki, shugaban Amurka Joe Biden ya yi Allah wadai da harin bama-baman da Iran ta kai ta sama a Isra’ila a jiya Asabar kuma ya ce sojojin Amurka da ke yankin sun taimaka wajen dakile kusan dukkan jiragen sama marasa matuki da makamai masu linzami” da aka harba Isra’ila, a zaman wani hari da ke barazanar kara ruruta wutar rikicin rikicin da aka kwashe watanni 6 ana yi a yankin Gabas ta Tsakiya.
Biden ya kuma ce ya tattauna da Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ta wayar tarho da yammacin jiya Asabar don "jaddada kudurin Amurka akan tsaron Isra'ila."
Biden ya ce yayin da basu ga wasu hare-hare a kan sojojin Amurka ko sansanoninsu ba a yanzu, za su ci gaba da sa ido akan duk wata barazana, kuma ba zasu bata lokaci wajen daukar dukkan matakan da suka dace don kare jama’arsu ba.
Dandalin Mu Tattauna