A jiya da rana shugaban Amurka Joe Biden ya katse bulaguronsa da yake yi a jihar Delaware zuwa fadar White House, domin tattaunawa da hukumar tsaro ta kasa a kan hare haren saman Iran kan Isra’ila, lamarin dake shirin dauke hankali a sa’o’i masu zuwa, a cewar White House a jiya Asabar.
Rukunin tsaron kasa yana bai wa shugaba kasa bayanai akai-akai a kan halin da ake ciki kana shugaban na tuntubar jami’an Isra’ila, haka zalika yake tuntubar kawayen Amurka, in ji kakakin hukumar tsaron kasa Adrienne Watson, yana fada a wata sanarwa.
Jiragen Iran marasa matuka sun nufi Isra'ila, in ji Press TV na kasar Iran mai yada labarai da harshen Ingilishi, yayin da ya ambato majiyoyin Iran.
Tehran ta lashi takobin daukar fansa kan harin da Isra’ila ta kai ta sama a harabar ofishin jakadancinta a Damacus, babban birnin Syria da ya kashe mutane 16 ciki har da wani babban kwamanda rundunar juyin juya hali na kasar dake zaune waje da wasu jami’ai 6.
A halin da ake ciki, Isra’ila tana zama cikin shirin ta kwana kana ta soke duk wasu harkokin karatu da na matasa.
Wata sanarwar ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin ya yi magana da ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant a kan daukar matakin gaggawa kan barazanar yankin.
Austin ya jaddada cikakken goyon bayan Amurka ga Isra’ila daga duk wani hari da Iran ko kawayenta zasu kai mata.
Dandalin Mu Tattauna