Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Cigaba Da Kai Munanan Hare Haren Da Ba A Taba Kaiwa Ba A Zirin Gaza


Gidajen da kuka kone daga barin wuta ta sama da Isra'ila ta kai kan Gaza
Gidajen da kuka kone daga barin wuta ta sama da Isra'ila ta kai kan Gaza

A yau Talata Isra'ila ta kai munanan hare-hare ta sama babu kakkautawa a zirin Gaza.

Lamarin da ba a taba gani ba a cikin shekaru 75 na rikicin da Falasdinawan, inda ta shafe dukkanin gundumomin kurmus suka zama kura duk kuwa da barazanar da Hamas ta yi na kashe kowane mutum da ta kama idan aka lalata gida.

Isra'ila ta sha alwashin daukar fansa mai girma tun bayan da kungiyar Hamas ta lalata garuruwanta, lamarin da ya bar tituna cike da gawarwaki a wani hari mafi muni a tarihinta.

Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu

Ta kira dubun dubatar sojojin jira ko-ta-kwana tare da yiwa Gaza kawanya, garin dake da al’umma miliyan biyu da dubu dari uku.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce adadin wadanda suka mutu a harin na Hamas na ranar Asabar ya kai 900, akasari fararen hula ne aka kashe a gidaje.

An kai ‘yan Isra’ila da dama da kuma wasu ‘yan kasashen waje zuwa Gaza a matsayin wadanda ake garkuwa da su.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce hare-haren ramuwar gayya da Isra'ila ta kai ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 770 tare da jikkata sama da wasu 4,000. Barin wuta da ake yi ta sama, wadda ita ce mafi muni da aka taba yi, ta tsananta a daren ranar Talata, inda ta girgiza kasa tare kana wuta da hayaki suka turnuke sararin sama tun da safiya.

Zirin Gaza
Zirin Gaza

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutanen Gaza 180,000 ne suka rasa matsuguni, da dama sun yi cunkuso a kan tituna ko a makarantu. Harin bama-bamai ya yi sadiyar rufe hanyoyin zuwa ga ma'aikatan gaggawa.

Ala Abu Tair mai shekaru 35, wanda ya nemi mafaka a can tare da iyalansa bayan ya tsere daga Abassan Al-Kabira da ke kusa da kan iyaka ya ce "An samu adadin shahidai da ba a saba gani ba, har yanzu mutane na karkashin baraguzan ginin, wasu abokai sun yi shahada ko kuma sun samu raunuka." "Babu wani wuri mai kariya a Gaza, kamar yadda kuke gani suna kai hari a ko'ina."

Radwan Abu al-Kass, mai horar da dambe kuma mahaifin ‘ya’ya uku, ya ce ya kasance daya daga cikin mutane na karshe da aka kwashe cikin benensa mai hawa biyar da ke gundumar Al Rimal bayan an kai wa yankin hari. A karshe ya sami ficewa a daidai lokacin da makami mai linzami ya afkawa ginin.

Makami mai linzami na Isra'ila ya afkawa wasu gini a Gaza
Makami mai linzami na Isra'ila ya afkawa wasu gini a Gaza

"An share gundumar baki dayansa," in ji shi.

An kashe 'yan jaridan Gaza su uku a lokacin da makami mai linzami na Isra'ila ya afkawa wani gini yayin da suke wajen ginin suna ba da rahoto, lamarin da ya kai adadin 'yan jaridar da aka kashe zuwa shida.

A Isra'ila, har yanzu ba a sami cikakken adadin wadanda suka mutu da wadanda suka bace a harin na ranar Asabar ba. A garin Be'eri da ke kudancin kasar, an debo gawarwaki sama da 100.

"Abin da na fi so shi ne in farka daga wannan mafarki mai ban tsoro," in ji Elad Hakim, wani wanda ya tsira daga wani bukin wake-wake da Hamas ta kashe mutane 260 yayin da suka halarci bukin da asuba.

Matakin na gaba da Isra'ila za ta dauka na iya zama hari ta kasa a zirin Gaza, yankin da ta yi watsi da shi a shekara ta 2005, kuma ta ci gaba da killace shi tun lokacin da Hamas ta karbi mulki a can a shekara ta 2007. Kawanyar da ta sanar a ranar Litinin za ta toshe hatta abinci, ruwa da man fetur daga isa yankin.

Kakakin rundunar sojin Isra'ila Rear Admiral Daniel Hagari ya ce, 'yan kungiyar Hamas ba su da wani wuri da za su buya a Gaza. "Za mu samo su a duk inda su ke."

HAMAS
HAMAS

Harin na ranar Asabar din da ta gabata, ya zo wa Isra'ila ne ba-zata, wanda ya dauki fiye da kwanaki biyu kafin a rufe katangar fasahar da aka gina da biliyoyin daloli, da ba za a taba iya kutsawa ba.

Yanzu shugabanin Isra'ila za su yanke shawara ko za su takaita ramuwar gayya don kare mutanen da aka yi garkuwa da su. Kakakin kungiyar Hamas, Abu Ubaida, ya fitar da barazana a ranar Litinin din da ta gabata cewa za su kashe dan Isra'ila daya da ke tsare ba tare da gargadi ba ga duk ko wani harin bam da Isra'ila ta kai kan wani gidan farar hula - kuma za su yada kisan.

Kasashen yamma sun bada cikakken goyon baya ga Isra'ila. Garuruwan Larabawa sun yi zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa. Iran, babbar mai taimakawa Hamas, ta yi murnar hare-haren amma ta musanta cewa tana da hannu a cikin lamarin.

~ Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG