Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Republican A Malajisar Dattawa Ya Amince Da Zaben Biden


Joe Biden
Joe Biden

A jiya Talata zababben shugaban Amurka Joe Biden ya ce ya fadawa shugaban ‘yan Republican masu rinjayi a majalisar dattawa Mitch McConnell yayin wata hirar waya cewa koda suna da sabani a kan abubuwa da dama, amma kuma zasu iya yin aiki tare a kan wasu abubuwa.

McConnell, da yaki bayyana amincewar sa ga nasarar Biden a baya, ya fada a wani jawabin majalisar dattawa jiya Talata cewa kuru’un wakilai 306 da Biden ya samu a kan kuru’u 232 ya tabbatar da nasarar sa na samun wa’adin shekaru hudu a fadar White House.

Ya zuwa wannan safiya, kasar mu ta samun zababben shugaban kasa da zababbiyar mataimakiyar shugaban kasa a hukumance, inji McConnell. Ya ce miliyoyi da dama a cikin mu na sa ran sakamakon zaben zai karkata wani wuri daban. Amma tsarin gwamnatin mu ya tanadi hanyar da za a tabbatar wanda za a rantsar a ranar 20 ga watan Janairu. Kuru’un wakilai sun raba gardama.

Trump da yake ci gaba da korafe korafe marasa tushe cewa an yi masa magudi a kokarin neman sake zabensa, bai maida martanin nan take a kan amincewar da McConnell ya yi cewa Biden ne zai zama shugaban Amurka na cikon 46.

A maimakon haka ya kafe wani sakon twitter cewa, an fitar da shaida masu tarin yawa dake nuna an tafaka magudi a zaben. Lamarin da ba a taba ganin irinsa ba a kasar mu.

Jim kadan bayan kalaman McConnell, Biden ya zanta da manema labarai a filin saukar jirage na jihar Delaware yayin da yake kan hanyarsa zuwa Georgia, ya ce ya kira shugaban masu rinjayi a majalisar dattawa, sun kuma yi tattaunawa mai ma’ana. Ya ce ya kira shi ne domin gode masa da ya taya shi murna.

XS
SM
MD
LG